Kano State Anthem, Taken Kano

Kano ita ce Jihata, Mu ne Jalla ta Hausa,
Fitila mai haskakawa,
Kano birni ga kowa, Ilimi har kasuwanci,

Mu ne gaba duk kasata
Kano zan ba da kai na,
Fansarki da rayuwata.

Kowa ya san ki Dala, Kano komai ka kawo,
ka tadda dubu-dubunsa

Kano tumbin giwa, Garin noma da kira.

Ba kamarmu fagen zumunei, Da karanci mu Kanawa
Kano ita ce madubi, A fuskar shugabanci,
Sarauta mun yi zarra.

Malamammu da tajiranmu,
Al’ada tarihinmu, Mu dai su ne adonnmu,

Su ne k.uma takamarmu,

Allahu Ka daukake mu (2x)
Mu ne Jalla ta Hausa
Kano tumbin giwa (2x)
Allahu Ka aukake mu
Mu ne Jalla ta Hausa.